Hukumar Zirga-Zirgar Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ta sanar da dawowar aiki jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna wanda aka dakatar sakamakon hatsari da ya yi a tashar Kubwa a makon da ya gabata, ranar Juma’a 27 ga watan Janairu, 2023.
NRC a cikin wata sanarwa, ta ambaci Daraktan Ayyuka, Injiniya Niyi Ali, na cewa jirgin zai dawo aiki a ranar Talata 31 ga Janairu 2023.
Jadawalin jirgin da aka fitar ya nuna jirgin farko daga Kaduna zuwa Abuja zai tashi da karfe 7 na safe yayin da jirgin farko daga Abuja zuwa Kaduna zai tashi da karfe 10 na safe.
Jirgi na biyu daga Kaduna zai tashi da karfe 1:00 na rana, yayin da jirgin Abuja zuwa Kaduna zai tashi da karfe 4 na yamma.
Sai dai a ranar Laraba jirgin kasa daya ne zai tashi daga Kaduna zuwa Abuja da misalin karfe 7 na safe sai kuma wanda zai tashi daga Abuja zuwa Kaduna da misalin karfe 4 na yamma.
“Muna nadamar duk wata matsala da fasinjojinmu masu suka fuskanta sakamakon matsala da jirgi ya samu ya samu.”
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1247 days 1 hour 31 minutes 4 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1229 days 3 hours 12 minutes 29 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com