Home General CBN yace bankuna zasu cigaba da karbar tsuffin kudi bayan wa’adi ya...

CBN yace bankuna zasu cigaba da karbar tsuffin kudi bayan wa’adi ya kare

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele ya ce bankunan ƙasar za su ci gaba da karɓar tsoffin takardun kuɗi daga hannun kwastomominsu har zuwa bayan wa’adin 10 ga watan Fabrairu, lokacin da za a daina amfani da tsoffin takardun kuɗin a ƙasar

Mista Emefiele ya bayyana hakan ne a lokacin da ya hallara a gaban kwamitin wucin-gadi kan sauya fasalin kuɗin ƙasar na majalisar wakilan ƙasar.

To sai dai gwamnan Babban Bankin bai bayyana lokacin da bankunan za su daina karɓar tsoffin takardun kuɗin ba.

Tun da farko dai kakakin Majalisar Wakilan ƙasar Femi Gbajabiamila, ya zargi gwamnan Babban Bankin da saɓa wa sashe na 20 na dokar CBN wadda a cewarsa ta wajabta wa bankunan ci gaba da karɓar tsoffin kudin har zuwa bayan wa’adin da Babban Bankin ya saka.

Yayin da yake jawabi a gaban kwamitin Emefiele, ya ce ya yarda da ‘yan majalisar game da sashe na 20 na dokar CBN.

”Sashe na 20 na cewa bayan cikar wa’adi za a daina amfani da tsoffin takardun kuɗi, to amma an wajabta wa bankuna karɓar ƙuɗaɗen. Dan haka ina tare da majalisa a kan haka”, in ji Emefiele.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Fiye da Kashi 60 na 'Yan Najeriya a Yanzu Suna Rayuwa Cikiin Fatara - IMFGwamnatin Najeriya ta Caccaki Afrika ta Kudu kan Harin da ake yi wa ƴan ƙasartaƳan Bindiga sun Buƙaci Kudin Fansa Kafin Sako Dattijan da Suka je Sulhu a ZamfaraMayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a Kano
X whatsapp