Home General El-Rufa’i ya Caccaki Wasu a Fadar Gwamnatin Tarayyar Nijeriya

El-Rufa’i ya Caccaki Wasu a Fadar Gwamnatin Tarayyar Nijeriya

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai yace akwai wasu “jami’ai” a fadar gwamnatin Najeriya ta Aso Rock a Abuja dake wa dan takarar shugaban kasar karkashin jam’iyyar APC mai mulkin Asiwaju Bola Tinubu, zagon kasa domin ya fadi zabe.

Da yake magana a wani shirin safe na gidan Talabijin na Channels, gwamnan ya ce wadannan mutanen da bai bayyana sunayensu ba suna cike da takaicin yadda Tinubu ya doke ‘yan takararsu a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC, abin da ya sa suka shiga shirya makarkashiya domin ya fadi zabe.

El-Rufai ya ce mutanen na fakewa ne da muradin shugaban kasa Muhammadu Buhari na yin abin da yake ganin ya dace.

“Suna kokarin ganin lallai sai mun fadi zabe, kuma suna fakewa da burin shugaban kasa na yin abin da yake ganin ya dace. Zan ba da misali guda biyu: wannan tallafin man fetur da ake kashewa tiriliyoyin Naira, tuni muka amince a janye”.

Malam Nasir El-Rufai yace yayi wata tattaunawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2021, inda ya nuna masa illar dake cikin ware sama da Tiriliyan 2 wajen biyan tallafin man fetur alhali kuwa ana kashe Naira biliyan 200 kacal a kasafin kudin gudanar da manyan ayyuka.

Yace shugaban kansa ya gamsu, hakan kowa dake cikin gwamnati ya amince da batun cire tallafin.

Misali na biyu da Gwamna El-Rufai ya bayar shine batun sauya fasalin wasu takardun kudin Najeriya Naira. Yace ana daurawa gwamnan babban bankin Najeriya CBN wannan laifi, amma kuma ba haka bane.

“Jama’a na zargin Gwamnan Babban Bankin ne da laifin sake fasalin kudin, amma ba haka batun yake ba, ku tuna da mulkin Buhari na farko a soji; wato gwamnatin Buhari da Idiagbon sun canza mana kudin mu kuma sun yi haka a asirce da nufin kamo wadanda ke wawure kudaden haram”.

Yace hakan mataki ne mai kyau, kuma hakkin sa ne, to amma yin hakan a wannan lokaci bashi da ma’ana a fuskantar tattalin arziki da siyasa.

Kalaman El-Rufai na zuwa ne mako guda bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyya mai mulki Asiwaju Bola Tinubu yayi zargin ana shirya makarkashiya don hanashi samun nasara a zabe mai zuwa ciki harda tsadar mai da kuma batun canjin kudi.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp