Home General CBN ya umarci dukkan bankunan kasuwanci na kasar da su fara biyan...

CBN ya umarci dukkan bankunan kasuwanci na kasar da su fara biyan masu ajiya a bankunan sababbin takardun naira

Babban bankin Najeriya CBN ya umarci dukkan bankunan kasuwanci na kasar da su fara biyan masu ajiya a bankunan sababbin takardun naira daga cikin bankunan ba kamar yadda ya umarce su da su rika biyansu ta na’urar cirar kudi ta ATM ba.

Wannan umarnin na zuwa ne bayan da harkokin kasuwanci suka kusan tsayawa cak bayan da gwamnatin Najeriya ta fitar da sababbin takrdun kudin na naira 200 da 500 da 1,000.

Cikin wata sanarwa da daraktan sadarwa na bankin Osita Nwanisobi ya sanya wa hannu, CBN ya lura da wasu miyagun halaye da ‘yan kasar ke nunawa na sayarwa da yin jifa da sababbin takardun kudin a iska da tattaka su yayin wasu bukukuwa.

Nwanisobi ya ce babban bankin ya hada gwiwa da rundunar ‘yan sandan Najeriya da hukumar tara haraji ta kasa da ta EFCC domin hukunta wadanda aka kama suna taka dokokin kasar, musamman wadanda suka jibanci yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa.

Bankin ya kuma gargadi ‘yan Najeriya da su guji halayyar wulakanta takardun kudin kasar musamman a yayin da suke bikin zagayowar ranar haihuwa da na aure da na binne mamata.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp