Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci yan kasar da su ba shi kwanaki bakwai kacal domin magance matsalolin kuɗi da ake fuskanta a kasar.
Shugaban ya bayyana haka ne a wani taro da ya yi da ƙungiyar gwamnonin Jam’iyyar APC bayan wata ziyara da suka kai masa domin neman mafita kan ƙarancin kuɗin da ake fama da shi waɗanda suka ce hakan na barazana kan ayyukan alkhairi da gwamnatin ta yi.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Malam Garba Shehu ya fitar, Shugaban ya ce sauya fasalin kuɗin da aka yi zai haɓaka tattalin arzikin ƙasar da kuma samar da tagomashi na tsawon lokaci ga ƙasar.
Haka kuma shugaban ya nuna damuwa kan lamuran wasu bankuna a ƙasar inda ya ce kansu kaɗai suka sani kuma a cewarsa ko shekara guda aka ƙara, matsalolin da suke tattare da san kai da zari ba za su gushe ba.
PRNigeria Hausa












