Ganduje yayi karar Buhari gaban Kotun Koli

Gwamnatin Jihar kano ta kai gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kara a gaban Kotun Kolin kasar a kan sauyin fasalin wasu daga cikin manyan kudin kasar na naira 200 da 500 da 1,000.
A karar wadda Babban Lauyan jihar ta Kano ya shigar ta hannun Sunusi Musa babban lauya a Najeriya (SAN), a ranar Alhamis, gwamnatin tana bukatar kotun ta ayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari shi kadai ba shi da hurumin umartar Babban Bankin Kasar, CBN ya dakatar da amfani da takardun kudin na naira 200 da 500 da kuma 1,000 ba tare da tuntuba da amincewar majalisar tattalin arziki da kuma majalisar zartarwa ta kasar ba.
A don haka ne gwamnatin jihar ta Kano take son Kotun ta soke matakin Babban Bankin na Najeriya na janye takardun kudaden saboda abin ta kira wahalar da al’ummar jihar ke ciki asaboda matakin na CBN.
Haka kuma gwamnatin tana son kotun ta bayar da umarnin da zai tilasta wa gwamnati ta soke shirin nata na sauyin kudi saboda a cewarta ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar na 1999.
A karar gwamnatin jihar ta Kano tana kuma bukatar Kotun Kolin ta zartar cewa umarnin da Shugaba Buhari ya bai wa Babban bankin Kasar na takaita yawan kudin da jama’a za su fitar daga asusunsu na banki ba tare da tuntubar majalisar tattalin arziki da kuma ta zartarwa ba, abu ne da ya saba wa tsarin mulki da saba wa doka a don haka ba shi da hurumi.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 17 hours 30 minutes 29 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 19 hours 11 minutes 54 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com