Adadin sojojin da suka mutu a sakamakon harin kwanton bauna da ‘yan ta’adda su kai musu a jamhuriyar Nijar ya kai 17 kawo yanzu.
Tun farko dai ‘yan ta’addar sun hari sojojin ne a garin Tillaberi dake kudu maso yammacin kasar gab da kan iyakar kasar da Mali, inda nan take suka kashe sojoji 13, wasu 16 kuma suka yi batan dabo.
Read Also:
Ma’aikatar tsaron kasar ta cikin sanarwar da ta fitar, ta ce kawo yanzu an tabbatar da mutuwar sojoji 17, sai wasu 13 da suka jikkata, yayin da har yanzu ake ci gaba da neman guda 12.
Wannan yankin dama ya jima yana fama da ayyukan ‘yan ta’adda, yayin da ayyukan kungiyar Al-Qaeeda da na IS ya ta’azzara musamman daga shekarar 2017.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1244 days 12 hours 21 minutes 12 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1226 days 14 hours 2 minutes 37 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com