Home Labarai An dage lokacin kidaya a Nijeriya

An dage lokacin kidaya a Nijeriya

Gwamnatin Najeriya ta sanar da jinkirta lokacin gudanar da Shirin kidayar jama’ar kasar da aka shirya yi a wannan wata na Maris zuwa watan Mayu mai zuwa.

Ministan yada labarai Lai Mohammed ya sanar da haka bayan wani taron majalisar ministoci a fadar shugaban kasa da aka gudanar ranar laraba.

Mohammed ya danganta dage shirin da jinkirta zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi da hukumar zabe tayi, abinda ya jirkita shirin hukumar kidayar.

Ministan yace majalisar ministocin Najeriya ta amince da bukatar hukumar na karbar kudin da ya kai naira biliyan 2 da miliyan 800 domin sayen na’urorin zamanin da za’ayi amfani da su wajen gudanar da aikin.

Rahotanni sun ce za’a gudanar da kidayar ce daga ranakun 3 zuwa 7 ga watan Mayu kamar yadda aka baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara.

Kidayar jama’a na daya daga cikin ayyuka masu sarkakiya a Najeriya saboda banbance banbancen dake tsakanin al’umma wadanda ake zargi da aringizon jama’a duk lokacin gudanar da irin wannan kidayar. Rabon Najeriya da gudanar da kidayar jama’a tun daga shekarar 2006.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Shin AtikuObi Zasu Iya Tsige TinubuShettima a 2027? Daga Yushau A. ShuaibYadda Shari'ar Masarautar Kano ke Ci gaba da Wakana a Kotun ta ƙoliTawagar Amurka na Shirin Tafiya Pakistan Domin Tattaunawar Sulhu da IranDole Najeriya ta Samu Tsaro ta Kowane Hali - Babban Hafsan TsaroChelsea da Newcastle na Harin Coulibaly, Liverpool na Neman Siyan Marcos SensiBadaƙalar $1.3m: Kotu ta ba EFCC izinin Kama Tsohuwar Ministar jin ƙan Najeriya Sadiya FarouqRaphinha ya Magantu kan Fitar da ƙungiyarsa da aka yi Daga Champion LigRundunar sojin Najeriya ta Musanta bai wa Tsofaffin Mayaƙan Boko Haram MakamaiGwamnatin Tarayya ta Sauya Zarge-Zargen da ta ke yi wa MalamiAn Binne Birgediya Janar Braimah da Sauran Sojojin da Boko Haram ta KasheYaƙin Iran: Hauhawar farashin Kaya a Najeriya ya ƙaruAdadin Matasa 'Yan kwaya da Muka Kama a Shekara 5 - NDLEAJam'iyyar ADC ta Kori Nafi'u Bala GombeRigakafin ƙyanda ya Ceci Yara Miliyan 20 a Afirka - Hukumar Lafiya ta Duniya2027 Ita ce Dama ta ƙarshe da zan Fito Takara - Atiku
X whatsapp