Mutune 5 sun mutu a wata arangama tsakani Mabiya Shi’a da Jami’an Tsaro

Musulmi mabiya darikar shi’a sun zargi gwamnan jihar Kaduna, malam Nasiru El’rufa’I da hallaka mabiya darikar mutum biyar.

‘Yan shi’ar sun zargi jami’an tsaron gwamnan da bude wuta kan mutanen yayin da suke gudanar da zanga-zanga a jihar kaduna ranar alhamis.

Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da sakataren harkokin ilimi na kungiyar Abdullahi Musa ya fita.

Haka kuma kungiyar tayi zargin lamarin nada alaka da kalaman tunzuri da Gwamnan yayi kwanaki kadan da suka gabata.

An ruwaito cewa mutane da dama sun sami raunika cikin su harda wadanda ke tafiya a gefen hanya yayin da lamarin ya auku.

Sanarwa ta kara da cewa “kwanaki kadan da suka gabata ne gwaman jihar kaduna, Malam Nasiru El’rufa’i, yayi wasu kalamai domin tunzura ‘ya’yan jam’iyyar sa a zariya akan mabiyar darikar shi’a da shugabanta Sheik Ibrahim Zakzaky (H), inda ya shaida cewa dole ne su zabi dan takarar sa Sanata Uba Sani domin ya gama da ragowar ‘yan shi’ar da suka rage a garin na zari’a.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 4 hours 36 minutes 1 second,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 6 hours 17 minutes 26 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com