Soja ya harbe wani matashi a jihar Kano

Rahotanni daga jihar Kano na cewa an harbe wani tsohon kansila a bisa zarginsa da sace akwatin kaɗa ƙuri’a.

Lamarin ya faru ne a yayin da ake gudanar da zaben gwamna da na ‘yan majaliasar dokokin jiha a ranar Asabar ɗin nan.

Rahotannin sun ce sojoji ne suka harbe Ibrahim Nakuzama, wanda tsohon kansila ne a mazaɓar Getso da ke ƙaramar hukumar Gwarzo.

Sai dai kawo yanzu rundunar sojan Najeriya ba ta kai ga fitar da sanarwa kan lamarin ba.

Wani makusancin mamacin ya ce tuni aka yi jana’izarsa a mahaifarsa a Getso.

Makusancin ya ce suna cikin jimamin rashin Ibrahim din, don haka babu wani bayani da zai ƙara. Ibrahim Nakuzama ya rasu ya bar mata biyu da ƴaƴa shida.

Ita ma a na ta ɓangaren, rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce ta kama mutane da dama saboda zargin tayar da hankali a lokacin zaben na ranar Asabar.

PRNigeria ta ruwaito cewa tuni matashin ya rigami gidan gaskiya, mu yi kokarin tuntubar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar kano amma bamu same shi ba.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 15 hours 6 minutes 42 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 16 hours 48 minutes 7 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com