Home Labarai Sojojin Nijeriya sun hallaka ‘yan bindiga 5 tare da kwato makamai a...

Sojojin Nijeriya sun hallaka ‘yan bindiga 5 tare da kwato makamai a jihar Kaduna

Dakarun sojojin Nijeriya runduna ta daya dake aiki a karamar hukumar Chikum a jihar kaduna, sun sami nasarar fatattakar ‘yan bindiga biyar tare da kwato bindigu kirar Ak-7 guda 6 da kuma gidan Alburusai na bindigar AK47 guda shida da kuma wani Alburushi masu tsayin 7.62mm guda 24.

Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mukaddashin mai Magana da yawun rundunar shiyya ta  daya Lt-Col Musa Yahaya ya fitar a jihar Kaduna.

Yahaya ya bayyana cewa dakarun sun gudanar da atisayen a yankin kan tudun Kaso da kanti zuwa Tantatu a dajin Kubusu dake jihar.

Yace atisayen ya kasance wani bangare na dakile ayyukan ‘yan fashi da masu aikata laifuka domin inganat tsaro da dawo da tattalin arziki mai dorewa a ‘yankin.”

Yahaya ya kara da cewa an fara atisayen ne a tsakar dare juma’a wanda ya sanya ‘yan bindigar suka jigata matuka.

Inda y ace sun sami nasarar kwato Babura hawa guda 3, wayar salula guda biyu da sauran kayayyakin amfani.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp