Home Labarai ‘Yan bindiga sun sace dalibai mata biyu na jami’ar Gusau

‘Yan bindiga sun sace dalibai mata biyu na jami’ar Gusau

‘Yan bindiga sun sace ɗalibai mata guda biyu a jami’ar tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara, arewa maso yammacin Najeriya.

Rahotonni sun ce ‘yan fashin ɗauke da muggan makamai, sun sace ɗaliban ne a ɗakunan kwanansu da ke wajen makarantar.

Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar ta fitar, ta ambato kwamishinan ‘yan sandan Zamfara, CP Kolo Yusuf na tabbatar wa iyayen ɗaliban da kuma hukumar makarantar cewa rundunar tana ƙoƙari don ganin ta kuɓutar da su.

Ta ce ‘yan sanda sun samu rahoton sace ɗaliban a ɗakunan kwanansu da ke a wajen makarantar, kuma ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, ta tura jami’anta zuwa wajen da lamarin ya auku.

Sai dai kafin zuwan jami’an tsaron ‘yan fashin sun tsere da ɗaliban, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Haka kuma sanarwar ta ce kwamishinan ‘yan sandan ya tura ƙarin jami’an tsaro don bin sawun ‘yan fashin da kuma kuɓutar da ɗaliban.

Zamfara, ta yi ƙaurin suna a matsayin jihar da ‘yan fashin daji suka mamaye wasu sassanta, inda suke kai hare-hare da sace mutane a ciki har wajen jihar suna neman kuɗin fansa daga makusanta da dangin waɗanda abin ya ritsa da su.

An yi imani har yanzu akwai ragowar daliban kwalejin tarayya ta Yawuri kimanin 11 dukkansu mata, waɗanda aka sato daga jihar Kebbi mai maƙwabtaka, kuma ake ci gaba da tsarewa a wani daji da ke cikin Zamfara wanda a yanzu sun kwashe kwanan 653.

Ranar 16 ga watan Yunin 2021 ne, ‘yan bindigar suka sace ɗaliban su kimanin 100 tare da wasu malamansu, inda suka tafi da su daji, kafin daga bisani su saki mafi yawansu cikin rukuni-rukuni.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp