Shirin Majalisar Ɗinkin Duniya na samar da abinci ya yi gargaɗin cewa akwai mutum miliyan 4.3 za su yi fama da matsananciyar yunwa a jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe, dukkansu a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Shirin ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar, game da wani rahoto da ya tattara kan matsananciyar yunwa a yankin ƙasashen kudu da hamadar Sahara.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Shirin na WFP ya nuna damuwa kan rikicin da aka kwashe shekaru ana yi da ‘yan bindiga zai iya jefa Najeriya cikin yunwa da tamowa, yayin da miliyoyin mutane suka dogara kan taimako da ake ba su na abinci, wanda kuma suke fuskantar barazanar faɗawa cikin yunwa.
“Kimanin mutum 600,000 na kan gabar faɗawa cikin wannan musifa.
Mutane za su fuskanci yanayin neman ɗaukin gaggawa saboda ƙarancin abinci, za kuma a fuskanci mummunar matsalar tamowa da mace-mace saboda ƙarancin kai kayan agaji,” in ji shirin.
PRNigeria hausa












