Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya tabbatar wa kwamishinonsa cewa za a tantance su bayan wata shida da kama aiki domin sanin waɗanda za su ci gaba da aiki da kuma waɗanda za a cire.
Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da majalisar zartarwar jihar ta yi zamanta na farko a ranar Laraba.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
A cikin jawabin da ya gabatar, Abba ya ce “Ina tunatar da ku cewa kuna da wata shida na gwaji bayan naɗa ku kan muƙami, bayan haka ne za a duba ayyukan da kowace ma’aikata ta gudanar, za a yaba wa waɗanda suka yi ƙoƙari sannan za a yi waje da waɗanda ba su yi ƙoƙari ba.”
Ana dai kallon matakin gwamnan matsayin wani sabon abu da ba’a saba ganin irin sa.
PRNigeria hausa












