Tsanani zai zama sauki Tinubu

Shugaban Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga al’umma, musamman matasan ƙasar da su ƙara haƙuri kan halin matsin rayuwa da suke fuskanta a yanzu.

Tinubu ya bayar da tabbacin cewa wahalhalun da ƴan Najeriya ke fuskanta a yanzu za su zamo daɗi a nan gaba.

Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a fadar gwamnatin ƙasar yayin da ya karɓi baƙuncin shugabannin matasa na jam’iyar APC daga jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Ya shaida wa matasan cewa gwamnatinsa za ta yi aiki tare da matasa a dukkan matakan da za ta riƙa ɗauka, ya kuma ƙara da cewa “ba zai yi shakkun ɗaukar kowane mataki da zai kawo ci gaba da haɗin kan ƙasa ba.”

Shugaba Tinubu ya ce ya fahimci irin raɗaɗin da ƴan ƙasar ke ciki “Na yi rantsuwa ga ƙasata cewa ba zan yi shakkar ɗaukar kowane irin matakin da zai samar da ci gaba da tabbatar da haɗin kan ƙasar nan ba.

“Matakan farfaɗo da tattalin arziki kan ɗauki lokaci kafin a fara ganin alfanunsu. Ku ƙara haƙuri kaɗan.”

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 15 hours 6 minutes 52 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 16 hours 48 minutes 17 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com