Home Labarai Rundunar ‘Yan Sandan jihar Adamawa ta tabbatar da aukuwar gobara a kasuwar...

Rundunar ‘Yan Sandan jihar Adamawa ta tabbatar da aukuwar gobara a kasuwar Yola

Gobara ta lalata wasu sassan babbar kasuwar garin Yola.

Rahotannin sun bayyana cewa go barar ta tashi ne  a daren Litinin yayin da yan kasuwar ke a rufe.

Wasu majiyoyi da dama sun ce shaguna da dama ne lamarin ya shafa, sannan gobarar ta yi sanadayar a sarar kayayyakin miliyoyin Naira.

Wani mazaunin da ke zaune a kusa da kasuwar ya ce, daukin gaggawa da jami’an kashe gobara suka yi ne ya ceci kasuwar daga barnar gaba daya.

Majiyar wadda ba ta fayyace musabbabin gobarar ba, ta ce kasuwar na da saurin barkewar gobara a duk shekara.

Hukumar kashe gobara ta jihar ba ta ce uffan ba kan lamarin, sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje ya ce an shawo kan lamarin.

Ya bayyana cewa nan take rundunar ‘yan sandan jihar ta samu rahoton barkewar gobarar, kwamishinan ‘yan sandan, CP Afolabi Babatola, ya tura karin jami,ai domin hana ’yan bata gari yin fashi a cikin kasuwar.
“Tare da goyon bayan ‘yan kwana-kwana, an shawo kan lamarin.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp