Majalisar Dattijai ta roki kungiyoyin kwadago kan tafiya yajin aiki

Ƙungiyoyin ƙwadago sun gabatar da rubutaccen saƙo ga Majalisar Tarayyar Najeriya, a wani ɓangare na zanga-zangar da ta gudanar ranar Laraba.

‘Yan ƙwadagon sun buƙaci shiga tsakanin ‘yan majalisar a dambarwarsu da ɓangaren zartarwa ko kuma su tsunduma yajin aiki a faɗin ƙasar daga ranar Alhamis.

Sai dai mai tsawatarwa, Sanata Ali Ndume, wanda shi ne jagoran kwamitin mutum da majalisar ta wakilta don karɓar masu zanga-zangar da suka je harabar majalisar a Abuja, ya roƙi ‘yan ƙwadagon a kan su jinkirta aniyarsu ta shiga yajin aiki daga Alhamis ɗin nan.

Ya buƙaci ƙungiyoyin ƙwadagon su bai wa Majalisar Tarayyar mako ɗaya a ƙoƙarinta na shiga tsakani don kawo ƙarshen wannan taƙaddama ba tare da durƙusar da harkokin gwamnati da na tattalin arziƙi a ƙasar ba.

Tun da farko, masu zanga-zangar ƙarƙashin jagorancin shugaban NLC babbar ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya, Kwamared Joe Ajero sun yi wa majalisar tsinke cikin rakiyar jami’an tsaro, a yunƙurinsu na ganawa da masu yin dokar.

Sai dai sun gamu da turjiya da farko daga jami’an tsaro, lamarin da ya kai ga karya ƙofar shiga harabar majalisar kuma dandazon masu zanga-zangar suka ɗunguma ciki.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 22 hours 50 minutes 39 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1237 days 32 minutes 4 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com