Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ya tabbatar da zaɓen Dakta Abdullahi Umar Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano, a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na ƙasa.
An zaɓi Ganduje ne a yayin taron kwamitin gudanarwar jam’iyyar na 12 da aka gudanar a otal ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja babban birnin ƙasar.
Shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu na cikin manyan ƙusoshin jam’iyyar da suka halarci taron kwamitin zartarwar APC na ranar Alhamis.
Haka zalika, kwamitin zartarwar ya tabbatar da Sanata Ajibola Basiru a matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa.
Read Also:
Bayan sanar da nade-naɗensu, magoya bayan Ganduje da Ajibola Basiru sun ɓarke da sowa da kuma murna waɗanda rahotanni suka ce har sun kusa hargitsa shirye-shiryen wurin na wani ɗan lokaci.
Ranar 17 ga watan Yuli ne tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu da babban sakataren APC Sanata Iyiola Omisore suka sanar da ajiye muƙamansu.
Daga bisani, jam’iyyar ta sanar da naɗin Sanata Abubakar Kyari, wanda shi ne mataimakin shugaban APC shiyyar arewacin ƙasar, a matsayin shugaban riƙo na jam’iyyar.
A ranar 27 ga watan Yuli ne shugaban ƙasar Bola Tinubu ya sanya sunan Sanata Abubakar Kyari cikin jerin mutanen da ya aika Majalisar Dattawan ƙasar don tantance su a matsayin ministocin gwamnatinsa.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 30 minutes 22 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 11 minutes 47 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com