Home Labarai Wani sabon hari a jihar Filato yayi sanadiyar mutane 21

Wani sabon hari a jihar Filato yayi sanadiyar mutane 21

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen  jihar Filato ta ce a ƙalla mutum 21 aka kashe a wani sabon hari da aka kai a ƙauyuka biyu a jihar.

Ƴan bindiga sun mamaye ƙauyen Barikin Ladi da sanyin safiyar Alhamis, inda suka harbe mutum 17.

Bayan wani ɗan lokaci an sake harbe mutum huɗu a wani harin da ƴan bindigar suka kai wani ƙauye da ke kusa da barikin ladin.

Kashe-kashen na zuwa ne a daidai lokacin da sojoji ke luguden wuta cikin dazukan da ke zargin maɓoya ce ta ƴan ta’adda a ƙoƙarin da gwamnati ke yi na kawo ƙarshen hare-haren da yayi sanadiyar mutuwar ɗaruruwan mutane tun daga watan Mayu.

Ƙungiyoyin fararen hula sun ɗora alhakin kashe-kashe kan makiyaya, inda suka ce suna yin hakan ne domin tarwatsa manoman yankin don samun damar mamaye filayensu.

Sai dai babu tabbaci ko ƙungiyoyin  makiyayan sun tofa albarkacin bakinsu kan wannan zargi.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp