Home Labarai KAROTA zata dauki mataki kan masu zaluntar Jami’anta a Kano

KAROTA zata dauki mataki kan masu zaluntar Jami’anta a Kano

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta jihar Kano KAROTA ta ce za ta bi kadin abinda wasu bata-gari suka yi wa jami’anta a karshen makon da ya gabata

Shugaban Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta jiha KAROTA Engr. Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana haka ta cikin wata takardar manema labarai da kakakin hukumar Nabilusi Abubakar Na’isa ya fitar mai dauke da kwanan watan 31/10.2023 aka kuma raba ga manema labarai a jihar Kano.

Yayin da yake duba biyu daga cikin jami’an  hukumar da ke kwance a asibitin Murtala da asibitin Kashi na Dala, Shugaban ya ce, ba zai zuba ido ya bari ana cin zarafin jami’an ba, a don haka ya bayar da tabbacin mika lamarin wajen jami’an ‘Yan Sanda domin fadada bincike tare da daukar matakin da ya kamata.

Haka Kuma, Tawagar shugaban Hukumar ta kai ziyarar Ta’aziyya ga jami’inta mai suna Nasiru Sani Abubakar a unguwar Yakasai Wanda Allah ya yi wa rasuwa sakamakon bige shi da mota ta yi; Ya yi Ta’aziyya ga iyalan jami’in tare da adduar samun gafara a gare shi da sauran alumma gaba daya.

Daga bias ya ja hankalin jami’an Hukumar da su ci gaba da gudanar da aikin su cikin kwarewa da mutunta jama’a.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp