Home Labarai Jirgin sojin saman Nijeriya ya yi hadari

Jirgin sojin saman Nijeriya ya yi hadari

Nigeria Airforce

Wani helikwaftan rundunar sojojin saman Najeriya ya yi hatsari a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas da safiyar yau Juma’a.

Mai magana da yawun rundunar, Edward Gabkwet ne, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce dukkan wadanda ke cikin jirgin sun kubuta, ko da yake sun samu “kananan raunuka”.

Jirgin helikwaftan kirar MI-35P ya yi hatsari ne da misalin karfe 7.45 na safe, jim kadan bayan ya tashi a kan hanyarsa ta zuwa yaki da masu zangon ƙasa ga tattalin arzikin kasa da ke fasasa bututu suna satar man fetur a jihar Ribas.

“Abin farin cikin shi ne dukkan ma’aikatan jirgin 5 sun kubuta da rayukansu, sai dai kananan raunuka kuma a halin yanzu ana kula da su a wani asibitin sojoji da ke Fatakwal.

“Babban hafsan sojojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar, a halin yanzu yana kan hanyarsa ta zuwa Fatakwal, don ganin halin da ake ciki da kansa, kuma da niyyar duba lafiyar ma’aikata,” in ji sanarwar.

ana ganin yawaitar hatsari da jiragen saman sojin Najeriya ke yi wanda ke janyo asarar rayuka, ya zama abin damuwa matuƙa a cikin shekara biyu, inda masu ruwa da tsaki suka yi kira ga sojoji, su kiyaye hanyoyin gudanar da ayyukansu da kuma kula da jiragensu na yau da kullum.

A watan Agustan 2023 ma, jirgin saman sojin Najeriya NAF MI-171 ya yi hatsari a kusa da kauyen Chukuba na jihar Neja, inda ya haddasa asarar sojoji.

A 2021, sojoji akalla 20 ne suka rasu cikin wata uku a hadurra uku na jiragen saman sojin Najeriya.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp