Home Labarai ‘Yan sandan Sun hallaka ‘yan bindiga 50 a Jihar Taraba

‘Yan sandan Sun hallaka ‘yan bindiga 50 a Jihar Taraba

rahotannin daga Nijeriya na bayyana cewa an hallaka ‘yan bindiga fiye da 50 da ake zargin su ne ke addabar karamar hukumar Bali ta Jihar Taraba.

Rundunar ƴan sanda a jihar ce ta bayyana haka ta bakin Kakakin ta Abdullahi Usman ta shaida hakan a ranar Alhamis cewa jami’an ‘yan sanda tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro ne suka kashe ‘yan fashin dajin.

Ya ce aikin hadin gwiwar ya zo ne bayan korafe-korafe da mutanen yankin suka yi wanda ya kai ga yi wa ƴan fashin kwanton bauna tare da halaka  su.

“Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta samu labarin cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, amma dai ana zargin masu garkuwa da mutane ne, daruruwan su sun kai farmaki kauyen Tonti da ke karkashin gundumar Maihula cikin karamar hukumar Bali a jihar Taraba.

“‘Yan bindigan sun kai farmaki kauyen ne da misalin karfe 5:30, kuma suka fara harbe-harbe,” kamar yadda ya shaida wa Channels.

“Da samun bayanai, kwamishinan ‘yan sandan Taraba, Joseph Eribo, ya bayar da umarnin tura wata zugar jami’an tsaro daga reshen Bali zuwa yankin ciki har da hadin gwiwar sojoji da ‘yan banga, da mafarauta.”

Ya ce suna ci gaba da farautar ‘yan ta’addan da suka tsere, kuma an tura wata runduna ta musamman domin inganta tsaro a yankin.

Sai dai ya kara da cewa: “Wani abin takaici shi ne ‘yan bindigan sun harbe mutanen yankin 12 kafin jami’an tsaro su isa”.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp