Tinubu Ya gana da Hafsoshin tsaron Kasar kan matsalar Tsaro

Shugaban Nijeriya Asiwajo Bola Tinubu ya gana da hafsoshin tsaron kasar da kuma wasu manyan hukumomin tsaro a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja, a ranar Talata.

Hafsoshin tsaron da suka halarci ganawar sun haɗa da babban hafsan tsaro, Janar Christopher Musa, shugaban rundunar sojin ƙasa, Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja, shugaban sojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar, da kuma shugaban sojojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla.

haka kuma mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu na cikin waɗanda suka halarci taron.

Sun tattauna kan batun karuwar aikata ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma kashe-kashe a faɗin kasar da nufin magance su.

Nijeriya dai na guda cikin kasashen yammacin Afirka dake fama da matsalar rashin tsaro, kama daga masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa dake cin karensu babu babbaka a yankin Arewa maso yamma da wasu jihohi a tsakiyar kasar.

sai kuma mayakan boko haram da na ISWAP dake tayar da kayar baya a yakin arewa maso Gabas, sai Kudu maso kudu da wasu yankuna a kudancin kasar dake fama da mayakan IPOB masu rajin kafa kasar Biyafara.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 18 hours 10 minutes 56 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 19 hours 52 minutes 21 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com