Home Labarai Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya aika sako zuwa ga Tinubu

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya aika sako zuwa ga Tinubu

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga Gwamnatin Tarayya data duba halinda Al’ummar Nigeria suke ciki na tsananin kunci kan hauhawar kayan abinci da rashin zaman lafiya a arewacin Kasar.

Sarkin yayi wannan kira ne a lokacin da Uwar gidan shugaban kasar Nijeriya Senator Remi Tunibu ta ziyarceshi a fadarsa dake gidan rumfa a jihar kano.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren masarautar Kano Abubakar Balarabe kofar Na’isa ya sanyawa hannu kuma aka raba ga manema labarai a jihar Kano

Alhaji Aminu Ado Bayero ya kara da cewa Senator Remi tayi kokari wajan fadada aikinta na alheri da takeyi a jahar kano dubada yawan Al’ummar da jihar take dasu.

Da take nata jawabin Uwar gidan Shugan kasar ta bayyanawa sarkin cewa tazo jihar kano ne domin tagodewa Al’ummar jihar bisa goyon bayan da suka bawa mijinta a lokacin zabe.

Daga karshe tayi alkawarin isar da sakon al’ummar Kano da Arewacin Nijeriya ga mai gidannata.

Uwar gidan shugaban kasar Senator Remi Tinubu tasamu rakiyar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa na kasa Senator Barau Jibrin da Gwamnan jihar Benue da matar shugaban majalisar wakilai na kasa da Uwar gidan Gwamnan Kano.

PRNigeria Hausa

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp