Hukumar kula da wutar lantarki a Najeriya ta amince da ƙara kuɗin wuta ga aboka hulɗarsu da ke ajin Band A – masu samun wuta tsawon sa’a 20 a rana.
Mataimakin shugaban hukumar, Musuliu Oseni ya bayyana cewa a yanzu kwastamomin za su biya N225 kan kowane kilowatt inda a baya suke biyan N66.
A taron manema labarai da aka yi a Abuja ranar Laraba, Oseni ya ce abokan hulɗarsa da ke samun wuta tsawon sa’a 20 a rana sune kashi 15 cikin 100 na kwastamomin hukumar a Najeriya.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ya ƙara da cewa hukumar ta kuma sauke kwastamomin da ke ajin Band A zuwa Band B masu samun wuta ƙasa da sa’a 20 a rana saboda rashin kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki na basu wutar da ta kamata.
Ya bayyana cewa ƙarin ba zai shafi kwastamomin da ke sauran matakan ba.
Tun bayan samun bayanai cewa hukumomi na iya ƙara kuɗin wuta ne, al’ummar Najeriya ke ta martani a shafukan sada zumunta inda wasu ke ganin matakin ya zo a lokacin da jama’a ke fama da tsadar rayuwa da kuma rashin tsayayyiyar wutar lantarki da ake fuskanta.
PRNigeria Hausa












