Home Labarai ‘Yan bindiga sun sace mata masu Juna biyu a jihar Katsina

‘Yan bindiga sun sace mata masu Juna biyu a jihar Katsina

Wani harin ‘Yan bindiga a garin Na-Alma dake  yankin karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina, yayi sanadiyyar batan mutane masu tarin yawa galibi mata har da masu juna biyu, da kananan yara, tare da kona gidaje,  da wani wanda ‘yan bindiga suka taba sare wa hannu da kafa, bayan kashe wani mai unguwa.

Rahotannin sun bayanai cewa, hare-haren ‘yan bindigan na baya-bayan nan sun jefa mutane da dama cikin tasku.

Wani mutumin yankin, wanda ya tsallake rijiya da baya ya ce suna cikin rudani, kuma kashi takwas cikin goma na mutanen garin sun yi kaura.

Mutumin ya kuma ce sun shaida wa jami’an tsaro cewa sun samu bayanan sirri na harin da ‘yan bindigar za su kai garin nasu.

“Tun wajen takwas da rabi na dare muka shaida wa jami’an tsaro amman ba su zo ba har sai da mutanen nan suka shiga suka fara harbi, sai dai kawai su ce ga su nan zuwa, amman ba su zo ba har sai da ‘yan bindiga suka gama kone-kone da duk abin da za su yi sannan suka zo.”

Jihar Katsina dai na guda cikin jihohin Arewacin Nijeriya dake fama da matsalolin rashin tsaro, duk da cewa mahukunta a jihar na bugun kirjin cewa sun daukar matakan da suka dace domin magance matsalar.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp