Shalkwatar tsaron Nijeriya ta ce sojojin da aka samu da laifi a kai hari kan masu mauludi a kauyen tudun biri na Jihar Kaduna zasu gurfana a gaban kotun hukunta sojoji domin fuskantar hukunci.
Daraktan yaɗa labarai na hedikwatar tsaron, Edward Buba ne ya bayyana haka a taron yaɗa labaran da aka gudanar a Abuja.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
inda yace Hedikwatar tsaron ta kammala binciken da aka daɗe ana dako kan bam ɗin da aka jefa kan mutane a ƙauyen Tudun Biri dake a ƙaramar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna.
A Disambar bara ne wani jirgin sojoji ya jefa bam kan mutanen da ke bikin maulidi lamarin da ya janyo asarar rayuka da jikkatar wasu da dama.
Rundunar sojin Najeriya ta ɗauki alhakin kai harin inda ta ce lamarin ya faru bisa kuskure.
PRNigeria Hausa












