Home General ISWAP ta Gargadi mazauna Kauyen Kukawa dake jihar Borno

ISWAP ta Gargadi mazauna Kauyen Kukawa dake jihar Borno

Mayaƙan ISWAP sun bai wa mazauna kauyen Kukawa lga sanarwar su bar kauyensu ko kuma su fuskanci kisa, kwanaki huɗu da hallaka masunta goma sha biyar a yankin Tumbun Rogo.

tunu wasu cikin mazauna kauyen suka fara guduwa sa’oi kadan bayan da suka sami wannan sanarwa kamar yadda jaridar Emergency Digest ta ruwaito.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaye sunansa, ya bayyana cewa mayakan sun tara jama’ar al’umma daban-daban a ƙaramar hukumar da sanyin safiyar Alhamis, inda suka ce su bar gidajensu kafin ranar Asabar, in ba haka ba za a kashe su.

A cewarsa, bayan da suka samu barazanar ‘yan ISWAP din, al’ummomin suka fara barin yankunansu, yayin da wasu suka tafi Kross Kauwa, wasu kuma suka tafi Monguno.

Kukawa lga ƙaramar hukuma ce a gefen tafkin Chadi wadda ta shahara wajen kamun kifi da noma, kuma akwai dakarun sojojin Najeriya da na ruwa.

Duk da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, mayaƙan Boko Haram/ISWAP na ci gaba da kai hare-hare a cikin al’ummomin

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp