Home DUNIYA Gwamnatin Jihar Sokoto ta Musanta cire Sarkin Musulmi

Gwamnatin Jihar Sokoto ta Musanta cire Sarkin Musulmi

Gwamnatin jihar Sokoto ta musanta zargin cire mai alfarma sakin musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III,

Wannan na cikin wata sanar wada mai Magana da yawun Gwamnan jihar Abubakar Bawa ya fita aka raba ta ga manema labarai, sanarwar kuma bukaci Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima ya rika bincike kafin yin sharhi kan duk Wani Labari da ya gani a kafofin sadarwa na zamani.

“Munyi zaton mataimakin shugaban kasa ya tuntubi Gwamnan Jihar sokoto kafin ya fito fili yayi magana akan Batun Tsige Sarkin Musulmi.

“gaskiyar magana ita ce, ba’a taba yunkurin tsige Sarkin ba, haka kuma ba mu aika masa da wata barazana ba dangane da hakan ba a cewar Sanarwar”

Sanarwar ta kara da cewa, Sarkin Musulmi na cin moriyar duk wani ikon da yake da shi, ba mu taba tauye masa wani ‘yanci ko hakkinsa ba”

Haka Gwamnati da al’ummar Jihar Sokoto na girmama Majalisar Sarkin Musulmi kuma zasu yi duk mai yiwuwa don kare martabar wannan Masarautar”.

Daga bisani gwamnati na tabbatarwa ‘yan Nijeriya cewa, za ta cigaba da kare Majalisar Sarkin Musulmi da mutuncinta a kowane lokaci”

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp