Home General NDLEA ta Bukaci yin Gwajin shaye-shaye kafin Aure a jihar Kano

NDLEA ta Bukaci yin Gwajin shaye-shaye kafin Aure a jihar Kano

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA reshen jihar Kano ta bukaci wajabta yin gwajin ta’ammali da miyagun kwayoyi kafin aure a jihar.

Kwamandan hukumar  Abubakar Idris Ahmad ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) a ranar Alhamis.

“A yunkurin hukumar na dakile dabiar ta’ammali da miyagun kwayoyi ta gabatar da wannan gwaji don kawar da dabiar daga Nijeriya,” a cewar sa.

Idris Ahmad yace gwajin zai zama wani mataki na magance shan miyagun kwayoyin da kuma kare wadanda basu fara ba daga cikin ma’auratan gami da wayar da kai da fadakar da su hadarin fadawa harkokin shaye – shayen.

Ya ce samar da dokar zai taimaka matuka wajen magance yawan mutuwar aure, gami da rage yawan matan aure dake shiga harkokin shaye – shayen a jihar.

daga bisani kwamandan hukumar ya bukaci wata da matasa da su guji dabi’ar shaye – shaye tare da bata hadin kai don kawar da ta’adar daga jihar da kasa baki daya.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp