Home DUNIYA Majalisar wakilai ta bukaci a gaggauta dakarar da yarjejeniyar Samoa

Majalisar wakilai ta bukaci a gaggauta dakarar da yarjejeniyar Samoa

Majalisar Wakilan Nijeriya ta bukaci gwamnatin Tarayya ta yi gaggawar dakatar da yarjejeniyar SAMOA da ta haifar da cece-kuce da zargin taba martabar addini da al’adun mutanen Nijeriya.

Majalisar ta kuma yanke shawarar bincikar yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta rattabawa hannu a ranar 28 ga watan Yuni.

An zartar da kudurin ne biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa na Ali Sani Madaki,  sashin  marasa rinjaye, da wasu ‘yan majalisa 87 suka dauki nauyi.

Kwanan nan yarjejeniyar ta haifar da cece-kuce saboda rahotannin cewa an shigar da tanade-tanade da suka shafi ‘yan madigo, ‘yan luwadi, bisexual, da transgender (LGBT) a cikin yarjejeniyar.

sai dai wannan na zuwa ne daidai lokacin da kungiyar lauyoyin kasar ta NBA da ake kallon matsayin masana doka suka fitar da sanarwar dake cewa cikin yarjejeniyar babu wani batun auren jinsi ko makamantan sa.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp