Shugaban kungiyar manoma ta AFAN, Arc. Kabir Ibrahim ya ce bada damar shigo da shinkafa Kasar nan barazana ne ga ‘yan Najeriya da suka zuba hannun jarinsu a kamfanunuwan shinkafa na gida.
Ya bayyana hakan ne yayin ganawa da jaridar Nairametrics a jiya Talata.
Read Also:
haka kuma ya yi kira ga gwamnati da ta zuba hannun jari ta hanyar bada tallafin kayayyakin noma kamar injina da taki da magunguna domin samun isasshen abinci a kasar.
“Nijeriya da ‘yan Nijeriya sun zuba hannayen jarinsu mai hawa a fannin samar da shinkafa, zai zama abin takaici gare su idan aka amince da shigo da shinkafa idan hakan ya zama dole”.
Hakan na zuwa ne yayin da gwamnatin tarayya ke shirin janye harajin shigo da kayayyakin abinci a dai-dai lokacin da kayan abincin ke tashin gwauron zabi a Nijeriya.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 16 hours 7 minutes 44 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 49 minutes 9 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com