Gwamnatin Jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya ta ce ta sami nasarar karbar tubabbun mayakan kungiyar boko haram 8,490 ta hanya shirin sabunta jihar Borno wato (Borno modern).
Kwamishinan yada labaran jihar farfesa Usman Tar ne ya bayyana hakan yayin da ake bawa tubabbun mayakan 560 rantsuwar tuba a birnin maiduguri a ranar laraba.
yace wannan sanannen al’mari ne ga dakarun sojojin da sauran jami’an tsaro dama masu rike da sarautun gargajiya a jihar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
yace shirin na tafiya yadda yakamata sannan kuma sun kama kwamiti domin bindiddigi, inda ya tabbatar da cewa wadanda suka tuban basa sake komawa ruwa tare da karya dokoki, sai dai suna komawa harkokin su na kasuwanci ne ma.
shima da yake jawabi a yayin taron mashawarci na musamman kan harkokin tsaro ga Gwamnan Jihar Birgediya Janar Abdullahi Ishaq (mai ritaya), ya tabbatar da adadin inda yace zuwa yanzu gwamantin jihar ta sami nasarar karbar tubabbun mayakan da suka kai 8,490, wanda hakan ya rage hadarin da al’ummar jihar ke fuskanta.
PRNigeria hausa












