Shugaban kasa Bola Tinubu ya kadu matuka bisa yadda wani gini a garin Jos dake jihar Filato ya fado kan daliban makarantar Saint Academy dake tsaka da daukar darasi.
Wannan na kushe ta cikin wata sanarwa da mai bawa shugaban kasar shawara kan harkokinyada labarai Ajure Ngelale ya fitar a yammacin ranar Juma’a.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Sanarwar tace Tinubu na mika sakon ta’aziyyar sa ga gwamnatin jihar Filato, Al’ummar da kuma iyayen wadanda iftila’in ya rutsa da su.
Tinubu ya bayyana wannan lamari matsayin wani rashe ga al’umma kasa baki daya.
Daga bisania ya umarci hukumar bda agajin gaggawa ta kasa NEMA, da kuma hukumar bata gajin gaggawar ta jihar Filato, jami’an tsaro da dukkan al’umma dasu bayar da gudunmawa wajen ceto wadanda wannan iftila’I ya rutsa da su.
PRNigeria Hausa











