Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa bazai saci dukiyar Al’ummar jihar kano ba, kuma bazai bari a satar musu kudi ba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yammacin asabar yayin da yake kaddamar da kasha na biyu na rabon tallafi ga Al’ummar kananan hukumomi 44 dake fadin jihar nan.
Abba ya bayyana cewa gwamnatinsa baza ta saci kudin al’ummar jihar ba, sannan kuma zata dauki matakin hukunta dukkan wanda ya saci kudin a karkashin kulawarsa.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Gwamnan yace zasu raba miliyan 260 ga mata 5,200 wadanda suka fito daga kananan hukumomin jihar 44, wanda kowacce zata sami naira dubu 50, wanda zai taimakesu wajen sanya jari.
Haka kuma yace zasu cigaba da taimakawa matan dake kananan hukumomin da naira miliyan 260 a dukkanin wata har zuwa karshen wa’adin mulkin sa.
Yace wannan na cikin kudirin su da kuma abinda suka yi al’ummar jihar alkawari a yayin yakin neman zabe, kuma wannan na matsayin sakayya da zasu yiwa mata bisa gudunmawar da suka bayar wajen kafa gwamnatin.
PRNigeria hausa











