Kudurin kirkirar sarakuna masu daraja ta biyu ya tsallake karatun farko a majalisar dokokin Kano
Sabon kudurin ƙirƙirar sakaruna masu daraja ta biyu ya tsallake karatu na farko a zauren Majalisar Dokokin Jihar Kano.
Sabbin Sarakunan da aka ƙirƙira dai sune na Rano, Ƙaraye da kuma Gaya.
A cewar ƙudurin, dukkansu za su kasance ne ƙarƙashin Sarkin Kano, wanda shi kaɗai ne mai daraja ta ɗaya yanzu a jihar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Kananan hukumomin da za su kasance ƙarƙashin Sarkin Rano sune Rano Kibiya da Bunkure, shi kuma na Karaye yana da kananan hukumomin Karaye da Rogo.
Matakin na zuwa ne bayan Majalisar ta rushe dokar da ta kirkiri sabbin masarautu guda biyar a jihar ta shekara ta 2019, tare da rushe sarakunan da aka naɗa musu.
Daga bisani dai Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya dawo da Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II kan kujerarsa, inda ya sauke Aminu Ado Bayero da sauran sarakunan guda hudu.











