Gwamnan jihar Kano Abba kabir Yusuf ya bayyana kaduwar sa bisa mutuwar ‘yan uwa da ‘yar kwamishinan ma’aikatar ilimi mai zurfi na jihar Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata. sakamakon iftila’in gobara.
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da darakta yada labaran Gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa PRNigeria, wadda ta ambaci gwamnan na nuna damuwa gami da kaduwa bias iftila’in gobarar da ya fada kan ‘yan uwan kamishinan mata guda biyu da kuma ‘yar sa.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Gwamnan Abba ya bayyana gobarar matsayin tashin hankali, wanda ya haddasa masa kaduwa duba da yadda ta kai ga rasa rayukan mutane 3 cikin al’ummar jihar kano, gami da rasa dukiya mai tarin yawa.
Sanarwa ta ce a madadin gwamantin jihar Kano, majalisar zartaswa, da al’ummar jihar Kano suna mika sakon ta’aziyya ga kwamishinan da ‘yan uwa da iyalai, tare da fatan Allah ya karbi shahadar su, ya kuma kiyaye aukuwar hakan anan gaba.
A ranar laraba ne dai Dr. kofara mata ya wallafa wani labara a shafin sa na Facebook, dake cewa gobara ta hallaka masa ‘yan uwan sa mata biyu tare da ‘yar sa guda daya.
A cewar sanarwar, ‘yarsa Maimuna (Islam) da babbar yayarsa Hajiya Khadija da matar dan uwansa Hajiya Juwairiyya sun rasu sakamakon gobarar da ta tashi.
PRNigeria Hausa











