Sakataren Gwamnatin tarayya, George Akume ya shiga ganawa da ministoci a yayin da ake shirin fara zanga-zanga kan tsadar rayuwa a fadin Najeriya.
Ganawar wacce ke gudana cikin sirri ta samu halartar ministoci sama da 40 na gwamnatin shugaba Tinubu.
Wasu daga cikin ministocin da aka hango a wajen ganawar sun hada da: Nyesom Wike na birnin tarayya Abuja da ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar da Zephnia Jisalo da Tahir Mamman da Atiku Bagudu.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Sauran ministocin sun hada da Wale Edun na kudi da ministan yada labarai Mohammed Idris da sauransu.
wannan dai na zuwa ne bayan, shugaban kasa Tinubu ya roki matasan Najeriya da su dakata daga shiga zanga zangar ta ‘EndBadGovernance’ da aka tsara farawa a wata mai kamawa.
ko da yake wasu wata kungiya da tayi ikirarin shirya zanga zangar tun da fari a Arewacin kasar ta janye yayin da wata kungiya kuma a jihar kano tace zanga – zanga babu fashi
PRNigeria Hausa











