Home Labarai Gwamnatin Kano ta magantu kan halin da ake ciki a jihar

Gwamnatin Kano ta magantu kan halin da ake ciki a jihar

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce ba za su saurarawa duk masu kokarin tayar da fitina da sunan zanga-zanga a fadin jihar kano ba.

Gwamnan ya furta haka ne yau a gidan Gwamnati Lokacin da yake karbar takardar korafi daga wasu jagororin al’umma kan dalilin da ya sa Suka fara gudanar da zanga Zanga a yau Alhamis.

Gwamnan ya kara da cewa duk da yake kudin tsarin mulkin kasa ya bayar da dama gudanar dazanga-zanga lumana ,amma gwamnati ba za ta zuba Ido wasu bata gari suyi amfani da ita ba wajen sace-sace kone-kone da fasa shagunan alumma, in da ya ce jami,an tsaro za su yi aiki ba sani ba sabo ga duk Wanda aka kama da hannu a ciki.

Gwamnan ya yabawa jami’an tsaro bisa yadda Suka jajirce wajen kakkabe batagari da ke Neman tayar da fitina a jihar kano.

Ya Kuma yabawa kungiyar da ta kawo takardar kokenta da cewa zai Jagorancin wasu daga cikin al’ummar kano har zuwa fadar Shugaban kasa don Mika sakonsu kan irin halin matsin da alumma ke ciki.

daga bisani  Gwamnan ya ja hankalin ‘ya siyasa da su guji yin amfani da bata gari don cimma bukatunsu

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp