Shugaban kasa Bola Tinubu na kallon yadda zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa ke gudana a fadin kasar nan.
Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Atiku Bagudu ne ya bayyana hakan yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin din channels.
Zanga-zangar da ake yi a kasar nan na da nasaba da tsadar rayuwa, da tabarbarewar farashin Naira da kuma cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ko da yake an yi ta kiraye-kirayen ga Tinubu ya yi jawabi ga al’ummar kasar bayan zanga-zangar ta shiga kwana na uku, amma har yanzu shugaba Tinubu bai yi hakan ba.
Sai dai Bagudu, ya ce shugaban na Nijeriya ya san halin da ake ciki sosai.
Kamar yada suma ministoci ke da nauyi a kan su, ya zame musu wajibi subi yada zanga-zangar ke gudana.
Ministan wanda ya amince da cewa ana shan wahala a kasar nan, amma gwamnatin tarayya na kokarin ganin an samu saukin rayuwa ga ‘yan kasar.
PRNigeria Hausa












