Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya (PDP) ta ce jawabin da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya gabatar a ranar Lahadi, game da zanga-zangar da ke gudana a faɗin ƙasar bai taɓo abubuwan da masu zanga-zangar ke kokawa a kai ba.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, wadda ta samu sa hannun sakataren yaɗa labarun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba, PDP ta ce “jawabin na Tinubu ya nuna yadda ƙarara, Jama’iyyar APC da shugaba Tinubu ba su damu da halin ƙunci da al’ummar ƙasar ke fama da shi ba.”
Tinubu dai ya yi jawabin ne kwana huɗu bayan da wasu matasa a Najeriya suka hau kan tituna domin nuna fushi kan halin matsin tattalin arziƙi da al’ummar ƙasar ke fama da shi.
A cikin jawabin da ya gabatar da safiyar Lahadi, Tinubu ya buƙaci al’ummar ƙasar su yi haƙuri su dakatar da zanga-zangar ganin cewa ta yi sanadiyyar rasa rayuka a wasu jihohin ƙasar.
Zanga-zangar wadda ta fara a ranar Alhamis ta rikiɗe zuwa rikici a wasu jihohin ƙasar, lamarin da ya kai ga asarar rayuka da dukiyar al’umma.
Read Also:
Sanarwar da PDP ta fitar ta ci gaba da cewa “Jam’iyyar ta yi takaicin yadda ya kasa bayyana ƙwararan matakan da ya kamata a ce gwamnati ta ɗauka domin kawo wa al’umma sauƙin matsin da suke ciki a ƙasar.
“Shugaban ƙasa ya kasa yin bayani kan buƙatun al’umma na ɗaukara matakan da za su rage tsadar man fetur da magance faɗuwar darajar naira da kuma samar da abinci ga al’ummar da ke cikin yunwa,” in ji sanarwar.
Shi dai Tinubu a jawabin nasa na ranar Lahadi, ya ce gwamnatinsa ta ɗauki matakai kamar na shirin bai wa ɗalibai bashin karatu, da raba wa jihohi maƙudan kuɗaɗe da kuma bayar da tallafin abinci ta hannun gwamnoni.
Sai dai masharhanta da dama sun soki jawabin na Tinubu, inda suka ce ya gaza taɓo buƙatun masu zanga-zangar kai-tsaye.
Kuma tuni ƙungiyoyin da suke jagorantar zanga-zangar suka lashi takobin ci gaba da gudanar da ita a yau Litinin.
Ƙungiyoyin kare hakkin bil’adama dai sun zargi jami’an gwamnati da bude wuta kan masu zanga-zanga, kuma sun buƙaci hukumomi su yi bincike a kai.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 23 hours 48 minutes 37 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 1 hour 30 minutes 2 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com