Fadar Shugaban Najeriya Bola Tinubu baya bayyana cewa zai yi tafiya zuwa ƙasar Faransa a yau Litinin.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
sanarwa bata bayyana dalilin ziyarar ba, amma ana sa ran Tinubu zai dawo Najeriya bayan wani dan lokaci kadan.
Wannan ziyarar ta biyo bayan ziyarar da ya kai kasar Equatorial Guinea a baya-bayan nan, inda ya gana da shugaban ƙasar Teodoro Mbasogo, inda suka yi shawarwari, da kuma sanya hannu kan yarjejeniyoyin man fetur da iskar gas, da kuma tsaro.
PRNigeria Hausa











