Home Labarai Jihar Kano ta sake rabauta da mukami a mulkin Tinubu

Jihar Kano ta sake rabauta da mukami a mulkin Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Farfesa Abdullahi Saleh Usman a matsayin shugaban hukumar kula da alhazai ta Nigeria (NAHCON).

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.

Farfesa Abdullahi Sale fitaccen malamin Addinin musulunci ne wanda ya yi digirinsa na farko a cibiyoyin ilimi na Musulunci guda biyu – Jami’ar Madina da Jami’ar Peshawar da ke Pakistan.

Ya kuma kware wajen gudanar da aikin Hajji, inda ya taba rike mukamin Shugaban Hukumar Jin dadin Alhazai ta Jihar Kano, kuma ya samu nasarar mai tarin yawa a lokacinsa.

Sabon mukamin nasa zai fara aiki ne bayan Majalisar kasa ta amince da nadin.

Shugaban ƙasar ya yiwa sabon shugaban hukumar ta NAHCON fatan alkhairi tare da fatan zai gudanar da aikinsa bisa gaskiya da rikon amana ga alhazan Nigeria .

Idan dai za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito ana zargin tsohon shugaban hukumar ta NAHCON Jalal Arabi da almundahanar kudade bayan kammala ibadar aikin hajjin bana.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp