Akwai Barazanar fuskantar Ambaliyar ruwa a Kano – NiMet

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet), ta yi gargaɗin samun ambaliya a wasu jihohin ƙasar sakamakon mamakon ruwan sama da za a samu kwanan nan.

Hukumar ta ce jihohin da suka haɗa da Kano, da Katsina, da Zamfara, da Jigawa da Kebbi da Kaduna, da kuma jihar Adamawa na cikin barazanar fuskantar ambaliyar ruwa, don haka ne ta yi kira ga mahukuntar jihohin su ɗauki matakan kare al’ummominsu.

uni dai dama ambaliyar ta fara ɓarna a wasu jihohin Najeriya inda aka samu asarar rayuka da ta dukiyoyi.

Alhaji Bashir Idris Garga, darakta a hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriyar NEMA ya ce wannan ruwan saman da za ayi na kwana uku ba ƙaƙautawa zai sanya magudanar ruwa da dama ba a cika damuwa da yashe su ba su cike wanda daga bisani ruwan zai malala har ya je yayi ɓarna.
“Saboda haka ya kamata a ɗauki mataki ƙwarai da gaske ya zama cewa ambaliyar bai yi ɓarna fiye da yadda ake zato ba.” daraktan ya ƙra da cewa.

Daraktan ya ce akwai irin wasu matakai da ake ɗauka na gaggawa irin su samun buhani a cika da yashi sai ayi tandagarƙi a canzawa ruwan akala yadda ba zai shiga yayi ɓarna ba.

Darakatan ya ƙara da cewa bayan haka, ya kamata a yashe magudanar ruwa sannan kuma a dage a sanar da ƴan uwa da abokan arziƙi cewa ga sanarwar da aka bayar kuma ya kamata a ɗau matakai.

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1183 days 23 hours 28 minutes 22 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1166 days 1 hour 9 minutes 47 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com