• Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Search
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Sign in
Welcome! Log into your account
Forgot your password? Get help
Password recovery
Recover your password
A password will be e-mailed to you.
PRNIGERIA PRNigeria Hausa
PRNIGERIA PRNIGERIA
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Home General Yadda Sojojin Najeriya suka kashe ƴanbindiga sama da 1,000 a Agusta
  • General

Yadda Sojojin Najeriya suka kashe ƴanbindiga sama da 1,000 a Agusta

By
'ƴan Bindiga
-
August 29, 2024
Arewa Award

Rundunar Tsaron Najeriya ta ce sojojinta sun kashe ‘ƴan bindiga sama da 1,000 a cikin wannan watan a faɗin Najeriya.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Rundunar Tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba, inda a ciki ya bayyana cewa aikace-aikacen sojin yana matuƙar daƙile ayyukan ƙungiyoyin ƴan bindigar.

“Muna sane cewa muna yaƙi ne da maƙiya marasa imani, wanda hakan ya sa dole mu ƙara ƙaimi wajen dakatar da su.”

Ya ce daga shirye-shiryen sojojin, akwai takura ƴan bindigar domin hana su sakat, “sannan sojojin suna bibiyar kwamandojin ƴan ta’addan da yaransu da ma masu taimaka musu.”

Ya ƙara da cewa tuni sun ga bayan wasu manyan kwamandojin ƙungiyoyin a watan “A Arewa ta Gabas an kashe irin Munir Arika da Sani Dilla (AKA Dan Hausawan Jibilarram) da Ameer Modu da Dan Fulani da Fari Fari da Bakoura Araina Chikin da Dungusu da Abu Darda da Abu Rijab.”

Read Also:

  • Gwamnan Kano Ya Kafa Runduna ta Musamman Don Tabbatar da Tsaro a Tashoshin Mota
  • NNPC ya fara bincike kan fashewar bututun mai a jihar Delta
  • Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin kisa kan Maryam Sanda

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa a yankin Arewa maso Yamma sojojin sun ga bayan manyan ƴan bindiga kamar su Kachalla Ɗan Ali Garin Fadama da Kachalla Ɗan Mani Na Inna da Kachalla Basiru Zakariyya da Sani Baka Tsine da Inusa Zangon Kuzi da Ibrahim da Tukur da Kamilu Buzaru da sauransu.

“Sojoji sun samu gagarumar nasara a kan ƴan bindigar, sannan kuma suna ci gaba da ƙara ƙaimi a aikace-aikacen da suke yi a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas domin magance matsalar tsaron da ake fama da su.”

Ya ce jimilla a watan Agusta, sojoji sun kashe ƴan ta’adda 1166, an kama guda 1,096 sannan an tseratar da waɗanda aka kama guda 721.

Haka kuma a cewar sanarwar, ak ƙwato makamai 391, da alburusai 15,234, sannan sun daƙile satar mai da aka ƙiyasta ya kai na Naira biliyan 5.

“Aikace-aikacen sojojin sun sa ƴan bindigar sun ja baya sosai, wanda hakan ya sa suke ta miƙa wuya, musamman a Arewa maso Gabas,” in ji shi, sannan ya ƙara da cewa sojojin za su ƙara matsa lamba a sauran yankunan domin samun irin wannan nasarar.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
  • TAGS
  • Agusta
  • Edward Buba
Previous articleSojoji sun hallaka ‘Yan Ta’adda 8 a jihar Kaduna
Next articleGwamnatin Najeriya ta bai wa ƴan kasuwa wa’adin rage farashin kayayyaki
'ƴan Bindiga

RELATED ARTICLESMORE FROM AUTHOR

NNPC ya fara bincike kan fashewar bututun mai a jihar Delta

Har yanzu sojojin Najeriya 11 na Burkina Faso – Tugga

Kwankwaso ya ce matsalar tsaro na neman fin karfin Gwamnatin Nijeriya

NDLEA ta cafke miyagun ƙwayoyi da darajarsu ta haura naira biliyan 6

KAROTA ta bukaci Al’ummar jihar Kano su bawa jami’anta hadin kai

Gwamnatin Neja ta ɗora alhakin sace ɗalibai kan makarantar

Kotu ta yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin daurin rai da rai

SAEMA 2025: IMPR Ta kaddamar da Littafi Kan Yaki da Sha da fatauci miyagun ƙwayoyi da fasa kwauri

Gwamnatin Najeriya ta dakatar da fara karɓar harajin man fetur

Majalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da Amupitan a matsayin shugaban INEC

NAHCON ta bayyana dalilian da suka saka Saudiya rage mata kujerun aikin hajji bana

Gwamnatin Najeriya ta cire darasin Lissafi cikin sharuɗan samun gurbin karatun Jami’a ga wasu ɗaliban

Recent Posts

  • Gwamnan Kano Ya Kafa Runduna ta Musamman Don Tabbatar da Tsaro a Tashoshin Mota
  • NNPC ya fara bincike kan fashewar bututun mai a jihar Delta
  • Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin kisa kan Maryam Sanda
  • Kotu ta tura tsohon ministan ƙwadago Chris Ngige gidan yari
  • Har yanzu sojojin Najeriya 11 na Burkina Faso – Tugga

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1642 days 3 hours 39 minutes 2 seconds,



Baptist School Students, Kaduna
1624 days 5 hours 20 minutes 27 seconds

Report By: prnigeria.com/hausa

Book on Sales: Boko Haram Media War: An Encounter with the Spymaster

boko haram

Click Here:To Order Now!

  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
© 2020 PRNigeria. All Rights Reserved.
Latest News
Gwamnan Kano Ya Kafa Runduna ta Musamman Don Tabbatar da Tsaro a Tashoshin MotaNNPC ya fara bincike kan fashewar bututun mai a jihar DeltaKotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin kisa kan Maryam SandaKotu ta tura tsohon ministan ƙwadago Chris Ngige gidan yariHar yanzu sojojin Najeriya 11 na Burkina Faso - TuggaNajeriya ta ce jirgin ta ya yi saukar gaggawa ne a Burkina FasoBurkina Faso ta tsare jirgin sojin Najeriya kan keta sararin samaniyar ƙasarKwankwaso ya ce matsalar tsaro na neman fin karfin Gwamnatin NijeriyaAn ceto wasu daga cikin daliban da aka sace a makarantar Papiri da ke jihar NejaAmnesty ba bukaci a gaggauta sakin Muhuyi MagajiAkwai sa hannun 'yan siyasa a kamen da aka yiwa Muhuyi - Gwamnatin KanoMajalisa ta amince da naɗin Chris Musa ministan tsaron NajeriyaWadanda aka sace a Cocin jihar Kwara sun shaki iskar 'yanciGwamnatin Nasarawa za ta kafa ƴan sandan JihaGwamnan Osun Ademola Adeleke ya fice daga jam’iyyar PDP
X whatsapp