Gwamnatin Najeriya ta yi barazanar riƙe albashin likitocin da ke yajin aiki

Ma’aikatar lafiyar Najeriya ta bayyana rashin jin daɗinta kan matakin da ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta Najeriya, NARD ta ɗauka na fara yajin aikin gargaɗi na kwana bakwai, duk da ƙoƙarin da gwamnatin ke yi na magance matsalolinsu.

A wata sanarwa da kakakin ma’aikatar, Ado Bako, ya fitar, ya ce gwamnatin ta sanar da aiwatar da dokar “ba aiki, babu albashi” na tsawon kwanakin yajin aikin, ma’ana gwamnati za ta riƙe albashin likitocin da ke yajin aiki har tsawon kwanakin da suka ɗauka suna yajin aikin, kamar yadda dokar ƙwadago ta tanada.

Bako ya jaddada cewa wannan matakin ba yana nufin yin watsi da halascin damuwar likitocin ba ne amma matakin na da nufin tabbatar da cewa muhimman ayyukan kiwon lafiya sun ci gaba da kasancewa ba tare da samun wata katsewa ba don amfanin jama’a.

Likitocin sun fara yajin aikin ne a ranar Litinin, domin matsa wa gwamnati lamba ta ceto abokiyar aikinsu, Dr Ganiyat Popoola da ke hannun masu garkuwa da mutane tun cikin watan Disambar shekarar da ta gabata.

Bako ya ƙara da cewa, ma’aikatar tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro, sun dukufa wajen ganin an sako Dakta Popoola, kuma a halin da ake ciki, akwai tattaunawa mai ƙarfi da ake yi don ganin a kuɓutar da ita daga hannun masu garkuwa da mutanen.

Ma’aikatar ta buƙaci likitocin da su koma kan teburin tattaunawa, inda ta jaddada muhimmancin samar da haɗin kai da kuma dawwamammen mafita kan ƙalubalen da ke fuskantar fannin kiwon lafiya a Najeriya.

Sanarwar ta sake jaddada aniyar ma’aikatar na yin tattaunawa mai ma’ana tare da yin aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki domin cimma maslaha mai dorewa.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 9 hours 29 minutes 53 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 11 hours 11 minutes 18 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com