Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari ƙauyen Mafa a ƙaramar Hukumar Tarmuwa da ke jihar Yobe a arewacin Najeriya, inda suka kashe mutanen da har yanzu ba a san yawansu ba.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya rawaito cewa, maharan sun yi sace-sace da yawa tare da banka wa shaguna da gidaje wuta a ƙauyen.
rundunar ‘yan sandan jihar ta bakin Kakakinta Dungus Abdulkarim ta tabbatar da faruwar lamarin a yau Litinin.
“Har yanzu muna aiki ne domin tabbatar da adadin mutanen da suka rasu dalilin wannan hari, wanda aka kai a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 4 na yamma.
“Wasu mutane da ake kira Babagana Goni da Bako Ibrahim ne suka shigar da ƙorafi kan harin a ofishin ‘yan sanda da ke Tarmuwa, kuma dukansu mazauna yankin Mafa ne.
“Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne ɗauke da makamai sun kai hari yankin Mafa a kan babura su sama da 50 kuma sun cinna wa shaguna da gidaje da yawa wuta.
Maharan sun kashe mutane da dama, amma har yanzu ba mu ƙididdige adadin waɗanda harin ya shafa ba,” in ji kakakin ‘yan sandan.
Ya ce bayan sun gama kai harin sun bar wasu makamai da rubutun larabci a jikinsu.
A ranar Juma’a NAN ya rawaito cewa, wasu ‘yan bindiga sun kai hari wata makaranta da ke kusa da garin Geidam tare da kashe ɗalibai uku da jikkata ɗaya.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 17 hours 54 minutes 59 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 19 hours 36 minutes 24 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com