Home General Jihar Kano na Sahun gaba wajen Mace-Macen mata masu Juna Biyu

Jihar Kano na Sahun gaba wajen Mace-Macen mata masu Juna Biyu

Shugaban kungiyar dake rajin kare hakkin Dan Adam da wayar da kai (CHRICED) Dakta Ibrahim M Zikirullahi ya bayyana cewa, Jahar Kano na kokari wajen tabbatar da an samu Cigaba mai dorewa a fannin lafiya ta bangare Samar da doka akan rage mace mace mata Masu juna biyu da kananan yara tun lokacin Tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso a shekarar 2001.

Dakta Ibrahim ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai da kuma kungiyoyi Masu zaman kan su kan Samar da hanyoyin magance matsalar yawan mace-mace mata Masu juna biyu da kananan yara ta Samar da dabaru don zantar da dokar haihuwa kyauta.

Kididiga na nuna cewa, jihar Kano na Cigaba da zama a sahu farko wajen samun yawan Mace -mace mata Masu juna biyu da kananan yara a kasar, Wanda haka ya zama barazana ga fannin lafiya a kasa.

Dakta Ibrahim ya Kara da cewa, rashin zartar da dokar haihuwa kyauta a asibitocin mu na Kara yawan mace-mace mata Masu juna biyu da kananan yara.

Hakazalika, zartar da dokar zai Kara bawa kananon asibitocin da ke a matakin farko Samar Samu kulawa tare da horar da likitoci da kuma Kara inganci aikin su .

Tabbas Gwamnoni da ake yi a Kano sunyi kokari wajen Samar da Dokar Wanda har yanzu wasu jahohin na matakin farko,sai dai zartar da dokar a jahar na zama tsaiko idan ka ga yadda kididiga ke nuna wa tun bayan kaddamar da dokar a watan mayu shekarar 2023.

PRNigeria Hausa

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp