Kamfanin NNPCL ya magantu kan karin farashin Man fetur a Nijeriya

Kamfanin mai na Najeriya NNPC ya ce man  fetur da kansa ne zai nemawa kansa farashi a kasuwa.

A wata tattaunawa da aka yi da mataimakin shugaban kamfanin na ƙasa Mista Adedapo Segun, ya ce kundin tsarin mulki bai ƙayyade waɗanda za su tsayar da farashin man fetur ba.

A cewarsa, sashe na 205 da ya kafa kamfanin, ya bashi damar sakin fetur don nemawa kansa farashi a kasuwa.

Ya ƙara da cewa dangane da tsadarsa da mutane ke kokawa, batu ne da ya shafi chanjin kuɗaɗe.

Amma ya ce su na ƙoƙarin su da dilallan man na ƙasa don ganin an magance karancinsa.

Kuma ya sake tabbatarwa da ƴan Najeriya cewar, nan da kwanaki kadan za a kawo ƙarshen matsalar ƙarancin man baki ɗaya.

A cewar kamfanin, a halin yanzu man fetur na nemawa kansa farashi ne a kasuwa.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 18 hours 14 minutes 22 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 19 hours 55 minutes 47 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com