Babban sifeton ‘yansandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya bayar da umarnin taƙaita zirga-zirga a jihar Edo a lokacin zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar ranar Asabar.
Cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yansandan ƙasar, Olumiyiwa Adejobi ya fitar, babban sifeton ya bayar da umarnin taƙaita zirga-zirgar ababen hawa a kan tituna da ruwa da sauran hanyoyin sufuri tun daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa 6:00 na maraice a ranar zaɓen.
To sai dai sanarwar ta iyakance masu muhimman ayyuka, ciki har da ‘yan jaridar da aka tantance da jami’an zaɓe da motocin ɗaukar marasa lafiya da masu kai ɗaukin gaggawa.
”Domin tabbatar da sahihancin zaɓen, babban sifeton ‘yansandan ya haramta wa duka jami’an tsaron da ke tsare ko raka manyan mutane zuwa rumfunan zaɓe ko cibiyoyin tattara sakamakon zaɓen”, kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.
Haka kuma sanarwar ta haramta aikin jami’an tsaron sa kai a faɗin jihar a lokacin zaɓen, haka kuma an haramta jiniya ga ababen hawan da ba a amince wa ba, domin tabbatar da kwanciyar hankalin masu zaɓe.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 22 hours 17 minutes 17 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 58 minutes 42 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com